Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA a jihar Ribas, ta sake sabunta bincike domin cafke wani da ake zargin dillalin muggan kwayoyi ne, Izuu Isuofia bayan da abokansa suka kai wa jami’an hukumar hari domin dakile kama shi a Fatakwal.
A wata sanarwa da kakakin hukumar NDLEA reshen jihar Rivers, Emmanuel Ogbumgbada, ya fitar a jiya, ya ce kwamandan jihar, Ahmed Mamuda, ya tuhumi jami’an su da su “dauki dukkanin makaman da suka dace domin tabbatar da kama wanda ake zargin da kuma ‘yan tawagarsa tare da gurfanar da su a gaban kuliya,Vanguard ta rahoto.
KARANTA WANNAN LABARIN: NDLEA Tayi Ram Wata Mata Mai Ciki da Wani Gurgu Dauke Da Miyagun Kwayoyi
“Da yammacin ranar 14 ga watan Afrilu, 2023, jami’an hukumar NDLEA reshen jihar Rivers sun kai samame a wani wurin shan kayan maye a kusa da titin Odunze, Mile 3 Diobu, dake Fatakwal da wani da ake zargin dillalin miyagun kwayoyi ne, mai suna Izuu Isuofia, wanda aka fi sani da ‘50’. tare da dimbin tabar wiwi da yake dauke ita.
“Lokacin da ake kokarin kai wanda ake zargin zuwa motar sintiri, sai ya daga kararrawa tare da bijirewa kama shi, lamarin da ya haifar da rikici, kuma cikin ‘yan mintoci kadan wasu ‘yan daba masu yawan gaske suka far wa jami’an mu da kwalabe da duwatsu, sannan suka kubutar da wanda ake zargi wanda tuni an sanya masa ankwa da kuma fitar da abubuwan baje koli kafin zuwan tawagarmu ta baya.”
A wani labarin kuma, Hatsari Ne Fitowar Melaye A Matsayin Dan Takarar Gwamna __ Tsohon Mataimakin Gwamna
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kogi, Yomi Awoniyi, ya ce zaben fidda gwani na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kogi da akayi a ranar Lahadi bana gaskiya ba ne.
Tsohon Sanata mai wakiltar Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya yi nasarar lashe zaben fidda gwani da kuri’u 313, Awoniyi ya zo na biyu da kuri’u 77.