Wata budurwa ƴar ƙasar Kamaru mai zauna a Amurka ta halaka kanta ta hanyar rataya bayan saurayin ta ya rabu da ita ya koma wajen wata daban.
Wani ɗan rajin karen haƙƙin bil-adama ɗan ƙasar Kamaru, Bella Powers shinr ƴa bayyana hakan a ranar Laraba, 29 ga watan Fabrairun 2023 a wani rubutu da yayi a shafin sa na Facebook. Shafin Linda Ikeji ya rahoto.
KU KARANTA KUMA: Yadda PDP ta ɓarnatar da Biliyan 12.5 cikin watanni biyu – Wike
Bella yace budurwar wacce take rayuwa a Hyatsville, Maryland, ta ɗauki wannan mummunan matakin ne bayan ta gano cewa tsohon saurayin na ta ya shirya auren sabuwar masoyiyar sa a ranar 3 ga watan Yunin 2023.
Budurwar wacce ta fito daga yankin Ngie a Arewa maso Yamma na ƙasar Kamaru, itace ta ɗauki nauyin kawo tsohon saurayin nata wanda ya fito daga yankin Bangwa a Kudu maso Yamma na ƙasar Amurka daga Kamaru da kuɗin aljihun ta.
Bayan ya ga gari ya saba da birni kawai sai ya yanke shawarar rabuwa da ita saboda ta fice masa a rai.
Wannan cin amanar da yayi mata shine ya sanya ta kasa jurewa ta yanke ɗanyen hukuncin halaka kanta da kanta ta hanyar rataya.