Ƙungiyar Malaman Makarantun Kwalejojin Kimiyya da Fasaha ta Najeriya a ranar Talata, tace cigaba da gina Makarantun ‘Polytechnics’ a Najeriya na cigaba da zama ayyukan mazaɓu ga ƴan siyasa domin cika muradun su na siyasa.
Shugaban Ƙungiyar ASUP na Ƙasa, Anderson Ezeibe ya bayyana haka a Abuja a taron bita na wuni biyu da taken “makomar Kwalejojin Kimiyya da Fasaha a Najeriya” wanda ƙungiyar ta shirya.
Yace “bamu amince da cigaba da gina “polytechnic’ ko’ina ba, domin yana kawo tsaiko ga bayar da ilmin gaba da Sakandire ga ƴan Najeriya, domin na yanzu sun zama basa burge matasan Najeriya.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ƴan sanda sun ƙwato Laptop 75, da Motoci 7 daga wata dabar ƴan ta’adda a Abuja
“A halin yanzu makarantun polytechnic na Fama da rikicin tabbatar da iko da nagarta, domin har yanzu bamu gamsu da cewa alhakin da aka ɗora masu an sanya shi a tsarin bada ilmi na ƙasa.
“Har yanzu ɗaliban da muke yaye wa ba’a gamsu dasu ba, ana ci masu mutunci, a yayinda malamai a ɓangaren ba’a cika masu masu haƙƙin su, wanda wannan ne ya sanya ƙwararrun malamai ke barin makarantun.
A ɓangaren shi, tsohon Ministan Ilmi Malam Ibrahim Shekarau wanda shine shugaban taron, yace rashin yin dai-dai da gwamnati keyi shine yake haifar da rashin fahimta, har ya zuwa yajin aiki.
“Wata matsala dana sani wanda ita ke haifar da cigaba da yajin aiki shine rashin Shugabanci nagari.
Abinda ke faruwa shine an ƙirƙiri ƙungiyoyi domin inganta jindadin mambobin ta, da kuma inganta makarantu da dama dake ƙarƙashin su,” inji shi