Mutane biyu ne suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata sakamakon fashewar wani Bom a karo na biyu a kasar Uganda.
Fashewar ta afku ne kwanaki biyu kacal bayan wani harin da ya hallaka mutane biyu tare da jikkata wasu da dama a bakin titi a kofar shiga Kampala babban birnin kasar a ranar Asabar.
‘Yan sanda sun kira fashewar farko da na ta’addancin cikin gida.
Shugaban kasar, Yoweri Museveni, ya bayyana harin a matsayin ta’addanci, ya kuma yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta iya hukunta wadanda suka aikata laifin.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jami’an tsaro su Kama masu kaiwa Yan bindiga Gas a Gusau
Sai dai rundunar ‘yan sandan Uganda ta dage cewa, mutum daya ne ya mutu a harin bam na biyu da aka kai a Kampala.
Rundunar ‘yan sandan ba ta bayar da cikakken bayani kan musabbabin fashewar Bam din ba.
“An killace wurin har sai an kammala tantancewa da bincike daga kwararrun bam. Za mu ba da bayanai lokaci-lokaci game da lamarin.” Inji Rundunar Yan sandan.
Sai dai har kawo hada wannan rahoton Babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai wadannan harin bama-bamai biyu