Majalisar Gudanarwa ta Jami’ar Jihar Gombe (GSU) a ranar Alhamis ta umurci dukkanin Ma’aikatan Makarantar da su koma bakin aiki cikin gaggawa.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata takarda ta cikin gida mai dauke da kwanan watan 2 ga watan Satumba mai dauke da sa hannun magatakardar jami’ar, Dr Abubakar Aliyu Bafeto.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hisbah A Zamfara ta yunƙuro kan yaƙi da Ƴan bindiga, ta haɗa hannu da NSCDC
Ya ce hukumar ta cimma wannan matsayar ne bayan taron gaggawa na ta karo na biyu da aka gudanar jiya, inda ya kara da cewa an samar da rajistar halartar jami’o’in da ke kula da ma’aikata (HODs) ga malaman da ke son komawa karatu.
Bafeto ya sanar da cewa, Hukumar gudanarwar jami’ar za ta sanya Dokar ‘Ba-Aiki, Ba-Kuɗi,’ ga duk Ma’aikatan da suka kasa komawa aiki nan da ranar 9 ga Satumba.
“Saboda haka, Hukumar Gudanarwar jami’ar na son sanar da dukkan ma’aikatan jami’o’in da wannan bayanin cewa majalisar gudanarwar a taronta na gaggawa na biyu da ta gudanar a ranar Alhamis, 1 ga Satumba, 2022, ta tattauna kan ɗage Yajin Aiki da Ƙungiyar Ma’aikatan jami’o’in suka fara (ASUU) kamar yadda ta shafi Jami’ar Jihar Gombe.
“Bayan kammala tattaunawa, majalisar ta yanke shawara tare da ba da umarnin cewa dukkan ma’aikatan ilimi su koma bakin aiki nan take. An ba da rajistar halarta a ofisoshin Shuwagabannin Sassa ga waɗanda ke shirye kuma suna shirye su ci gaba da koyarwa, ”in ji sanarwar.
Daily Trust ta ruwaito cewa, a ranar 22 ga watan Agusta ne hukumar Jami’ar Gombe ta koma gudanar da harkokin karatun dalibai na mataki na 100. Jami’ar ta kuma sanya ranar 3 ga watan Satumba domin tantance sabbin daliban da suka samu gurbin karatu.
A wani labarin kuma: Nafi Shekaru 10 ina lalata da Ƙananan Yara — Wani Ɗan Shekara 57 da aka kama shi yayi lalata da Ƙaramar Yarinya
An kama wani mutum mai shekaru 57, mai suna Chidi Obieze a ranar Laraba bisa zarginsa da lalata wata yarinya ƴar shekara 10.
Mutumin wanda ya ce shi dan asalin Egbem Ozubulu ne a karamar hukumar Ekwusigo ta jihar Anambra, an kama shi ne a unguwar Oraifite da ke makwabtaka da ita, saboda yadda ya saba da lalata ƙananan yara.