Kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ta bukaci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gana da kwamitin da suka tattauna karkashin jagorancin Farfesa Nimi Briggs.
Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osekede ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.
Dimukoradiyya ta ruwaito cewa kwamitin Briggs wanda gwamnatin tarayya ta kafa a ranar 7 ga watan Yuni, shine zai sake tattaunawa da ASUU tare da mika rahotonsa ga ministan ilimi, Malam Adamu Adamu nan da watanni uku.
To sai dai shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce “gaskiya ya isa haka ajiye dalibai a gida.”
Ya bukaci Buhari da ya gana da tawagogin tattaunawa da kuma sanya hannu kan rahoton.
NAN ta ruwaito cewa ana sa ran kwamitin da Briggs ke jagoranta zai sake duba daftarin yarjejeniyar bangarorin.
Har ila yau, a sake yin shawarwari cikin gaskiya da kuma iya aiki da yarjejeniyar 2009 tare da wasu Ƙungiyoyin Jami’a; tattaunawa da ba da shawarar duk wani batu da kwamitin ya ga ya dace don sake sanya NUC don gasa a duniya; da kuma gabatar da daftarin yarjejeniyar cikin watanni uku daga ranar da aka kaddamar.
Kungiyar ASUU sun fara yajin aikin ne a ranar 14 ga watan Fabrairu, bayan da gwamnatin tarayya ta gaza biyan wasu bukatunta da suka hada da sakin kudaden farfado da jami’o’i, da sauran su.