Kungiyar malaman jami’o’i ta kasa (ASUU) ta ce ba za ta janye yajin aikin gargadi na wata daya da ta fara a ranar 14 ga watan Fabrairu ba.
Emmanuel Osodeke, shugaban kungiyar, a lokacin da yake magana da gidan Talabijin na Channels TV a ranar Litinin, ya jaddada cewa kungiyar ba za ta ja da baya kan yajin aikin ba, domin a kullum gwamnatin tarayya ta gaza cika alkawurran da ta dauka wa kungiyar a shekarun baya ta ke yi.
Kungiyar ta ce ba ta son alkawura daga bangaren gwamnati a wannan lokaci sai dai a dauki mataki.
“Shekaru tara ko fiye da haka suna yi mana alkawari amma da zarar an kammala yajin aikin sai su sake komawa. Don haka, abokan aikinmu sun gaji da waɗannan alkawuran da ba su cika ba. Abin da muke so shine kaddamarwa a zahiri”
Ya bayyana cewa makarantu da dama ba su rasa ko wace shekara ta karatu ba duk da yajin aikin da kungiyar ASUU ta yi, yana mai jaddada cewa mambobin kungiyar sun sadaukar da rayuwarsu wajen samar da ilimi a kasar nan.
Ya yi nuni da cewa malamai da dama ba su tafi hutu ba tsawon shekaru a yayin da suke kokarin ganin Jadawalin karatun jami’o’i Bai Sami Wata matsala ba, sabanin rade-radin da ake yi na cewa malaman Najeriya ba su yi komai ba.
Osodeke ya kuma bayyana cewa ana biyan malamai albashin aikin da aka yi, yana mai cewa duk wanda ya ce ASUU ana biyansu bayan yajin aikin, karya yake yi.
Ya kara da cewa da gwamnatin tarayya ta bi nasu bangaren da ASUU ba ta shiga yajin aikin ba.
Shugaban ASUU ya Kuma yi ammana da cewa daliban na da ‘yancin yin zanga-zanga a kan abin da suke ganin ba daidai ba ne, amma ya bayyana cewa kungiyar dalibai ta kasa (NANS) ba zata firgita ASUU ba.