By Abbas Yakubu Yaura
An shiga firgici a lokacin da wani abu da ake zargin na’urorin fashewa ne a daren Lahadi daya afku a wani otel da ke yankin Kabala ta Yamma a karamar hukumar Kaduna ta Kudu a cikin birnin Kaduna.
Shaidun gani da ido sun ce sun ji karar fashewa a harabar otal din Dorino da misalin karfe 9:00 na daren Lahadi.
Daya daga cikin majiyoyin, wani dan banga a yankin ya shaidawa majiyar jaridar Dimokuradiyya cewa ba a iya gano tushen fashewar bam amma jami’an tsaro sun ziyarci wurin domin gudanar da bincike kan musabbabin fashewar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Muhammed Jalige, ya shaida wa manema labarai cewa, abin da ya haddasa fashewar abu ne da ake kyautata zaton na IED ne.
Ya lura da cewa jami’an rundunar ‘yan sandan da ke yaki da bama-bamai sun kasance a wurin don nazarin barbashi fashewar a wurin.
Ya ba da tabbacin za a ba da cikakkun bayanan binciken bayan kammala bincike.
Sai dai Jalige ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba daga fashewar yayin da barnar da fashewar ta haifar kuma ba ta da yawa.
A cewarsa: “An yi zargin fashewar bama-bamai ne, ba a samu asarar rayuka a lamarin ba. Babu gawa a cikin ginin lokacin da ya fashe. Lamarin ya faru ne a daren Lahadi da misalin karfe 21:45 na dare.
“An tura rundunar da ke yaki da bama-bamai zuwa wurin domin tantance barbashin da muka samu daga wurin.”