By Abbas Yakubu Yaura
Alamu sun nuna cewa kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) sun kammala shirin tsawaita yajin aikin gargadi na watanni biyu.
Wani jigo a kungiyar ASUU ta kasa ya shaida wa Daily Trust a safiyar ranar Litinin cewa kungiyar ta kammala shirye-shiryen sake gina jami’o’in na tsawon akalla makonni 8 domin matsawa bukatar gwamnatin tarayya.
DUBA WANNAN LABARIN: Gwamna Ganduje, Sarkin Kano Sun Ziyarci Olubadan, Domin Kulla Kyakkyawar Alaka
“Zan iya gaya muku cewa har yanzu ana ci gaba da tattaunawa dangane da yajin aikinmu na gargadi, amma mai yiwuwa mun tsawaita yajin aikin da makwanni 8,” jami’in da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho.
Amma da aka tuntubi shugaban kungiyar ta ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana rahoton kan karin wa’adin a matsayin hasashe ne kawai, inda ya kara da cewa mambobin hukumar na ci gaba da tattaunawa kan matakin na gaba.
“Ba mu yi magana kan wannan batu ba. Hasashe ne kawai. Har yanzu dai ana ci gaba da tattaunawa kamar yadda nake magana da ku,” Farfesa Osodeke ya shaidawa manema labarai.
A halin da ake ciki kuma, da misalin karfe 6:50 na safiyar ranar Litinin, wata kungiyar ASUU da ba a tantance ba ta shafin ta na Twitter ta kuma bayyana cewa kungiyar ta tsawaita yajin aikin gargadi da makonni takwas.
Safin na Tweeter din ya kara da cewa, “YANZU-YANZU: ASUU ta tsawaita yajin aikin ta da makonni 8.Ku kasance da mu domin jin karin bayani. #ASUU #ASUUstrike.”
Jaridar Dimokuradiyya a baya ta rawaito cewa kungiyar ta shelanta yajin aikin gargadi na tsawon wata daya a ranar 14 ga watan Fabrairu, wanda wa’adin ya cika a yau.
A halin yanzu ‘yan Najeriya sun kosa su san matakin da za a dauka na gaba daga malaman jami’o’i da gwamnatin tarayya.
Batutuwa da dama da ‘yan kungiyar ASUU ke neman a zartar da su sun hada da: rashin aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna ta shekarar 2009 (MoU) da aka cimma da ita; karancin albashi ya haifar da shigar da tsarin IPPIS; farfado da jami’o’i a fadin kasar, da dai sauransu.
A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar ta caccaki gwamnati kan sanarwar da ta yi kwanan nan cewa Jami’ar (UTAS) ta fadi jarabawar tantance gaskiya.
Comments 1