ASUU tayi wani tsokaci game da cire jami’o’i daga tsarin biyan albashi na IPPIS
Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta mayar da martani ga umarnin gwamnatin tarayya na cire jami’o’i da sauran manyan makarantu daga tsarin biyan albashin ma’aikata na IPPIS.
Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce ci gaban zai dawo da jami’o’in kan turba idan abin da majalisar zartarwa ta ƙasa ta amince da shi ya yi daidai.
KARANTA WANNAN LABARIN:Za’a Kashe Miliyan 500 Don Gudanar Da Zaben Ƙananan Hukumomin Yobe – Inji Shugaban Hukumar
DAILY POST ta ruwaito cewa Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ya sanar da cire jami’o’i, kwalejojin kimiyya da fasaha da kwalejojin ilimi, da sauran manyan makarantu daga tsarin biyan kudin albashi na IPPIS.
An dauki matakin ne yayin taron majalisar zartarwa ta tarayya ranar Laraba.
Osodeke, wanda ya zanta da Daily Trust a ranar Larabar da ta gabata, biyo bayan cire manyan makarantu daga tsarin biyan kudi na albashi na IPPIS, ya yabawa gwamnati kan sauya tsarin.
“Idan hakan ya yi daidai, mataki ne mai kyau a kan hanyar da ta dace. Muna yabawa gwamnati akan hakan. Abin da muke magana a kai ke nan. Idan hakan yayi daidai, yanzu muna zuwa a matsayin jami’o’i a hankali
A wani labarin kuma:Ana Iya Kada APC a zaɓen 2027 – Inji Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar
Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na yankin Arewa maso Yamma, Dakta Salihu Lukman, ya yi gargadin cewa za a iya korar jam’iyya mai mulki a shekarar 2027.
Lukman ya yi wannan gargadin ne a ranar Larabar da ta gabata a Abuja yayin ganawa da manema labarai gabanin kaddamar da sabon littafinsa da aka shirya gudanarwa a ranar Talata mai zuwa.