Zargin damfarar dala biliyan 2.3: ‘A shirye nake in bayar da shaida a kotu’ – Obasanjo ya sanar da FG
Tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa a shirye yake ya bayar da shaida ga Najeriya game da tsohon ministan wutar lantarki da karafa, Olu Agunloye a kan dala biliyan 2.3 da ake takaddama a kai kan kwangilar samar da wutar lantarki ta Mambilla.
Kamfanin Sunrise Power da Najeriya sun yi takun-saka a cibiyar kasuwanci ta kasa da kasa da ke ICC da ke birnin Paris na kasar Faransa, yayin da kamfanin ke zargin karya kwangilar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ana Iya Kada APC a zaɓen 2027 – Inji Tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar
Sunrise Power ta ce gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ce ta ba ta kwangilar ginawa, gudanar da aiki da kuma canja wurin dala biliyan 6 a watan Mayun 2003.
Kamfanin dai na zargin gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi watsi da yarjejeniya tare da neman a biya ta dala biliyan 2.3.
Kamfanin ya kara da cewa tuni ya kashe miliyoyin daloli kan masu ba da shawara kan harkokin kudi da shari’a kafin a yi watsi da kwangilar.
Sai dai a nata bangaren gwamnatin Najeriyar na zargin zamba da almundahana da jami’an gwamnati wajen bayar da kwangilar.
A cikin wasikar da ya aike wa babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a Lateef Fagbemi, lauyan gwamnatin Najeriya, tsohon shugaban kasar ya bayyana aniyarsa ta bayar da shaida a madadin gwamnatin Najeriya “ta kowace fuska.
A wani labarin kuma:Za’a Kashe Miliyan 500 Don Gudanar Da Zaben Ƙananan Hukumomin Yobe – Inji Shugaban Hukumar
Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta mayar da martani ga umarnin gwamnatin tarayya na cire jami’o’i da sauran manyan makarantu daga tsarin biyan albashin ma’aikata na IPPIS.
Shugaban ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya ce ci gaban zai dawo da jami’o’in kan turba idan abin da majalisar zartarwa ta ƙasa ta amince da shi ya yi daidai.