Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya gana da kungiyar Editoci ta Nigerian Guild Of Editors.
Alhaji Atiku Abubakar Tare da tawagar sa ne suka isa wajen tattauna da kungiyar ta shirya wanda kuma wani bangare ne na ganin an fahimci irin manufofin sa.
KARANTA ANAN: Atiku Wazirin Adamawa Ya Shirya Samar Da Wani Shiri Don Ci gaban Najeriya
Ya bayyana cewa a yayin tattaunawar da suka yi, yayi musu bayani dangane da irin kudurorin sa na ganin ya farfaɗo da komaɗar Najeriya.
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa Tattaunawar ta kasance gwanin ban sha’awa domin ta kayatar da kowa, wanda aka rabu cike da farin ciki.
A wani labarin kuma: Da Dumi-Dumi: Yan sanda Sun Karbe Iko Da Majalissar Dokokin Jihar Ekiti
An rufe majalisar dokokin jihar Ekiti saboda jita jitar da ake samu dake nuna cewa, wasu mutane naa shirin mamaye majalissar.
Wakilin DAILY POST da ya ziyarci harabar majalisar ya ruwaito cewa jami’an ‘yan sanda na jibge a muhimman wurare a cikin harabar majalisar domin dakile duk wata barazanar tabarbarewar doka da oda.