Majalisar wakilai ta dage ci gaba da zaman majalisar zuwa ranar Talata 22 ga watan Nuwamba, domin ba da damar yin wasu gyare gyare a zauren majalisar. Kamar yadda Daily Trust ta ruwiato.
Magatakardar majalisar, Dakta Yahaya Danzaria ne ya sanar da dage zaman a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Atiku Abubakar Ya Hana Da Kungiyar Editoci Ta Najeriya
Magatakardar ya bukaci ‘yan majalisar da sauran jama’a da su yi watsi da ranar da aka sanya tun da farko na ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba da cigaba da zaman Majaissar, inda ya bayyana cewa, yanzu za’a a yi zaman ne a ranar Talata.
“An umurce ni da in sanar da ’yan uwa da sauran jama’a da su yi watsi da batun dawo da zaman majalisar da aka sanar a baya, na ranar Alhamis, 17 ga Nuwamba, 2022.
“Za a yi aikin sauran gyare-gyare da kuma sanya kujeru a cikin wannan makon.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN ya ruwiato cewa, “Yanzu an shirya ci gaba da zaman a ranar Talata, 22 ga Nuwamba, 2022, da misalin karfe 11:00 na safe.,” in ji shi.
A WANI LABARIN KUMA: Bayan Tafka Zazzafar Muhawara, Akarshe Majalissar Dattijai Ta Goyi Bayan CBN
Majalisar dattijai ta kuduri aniyar bayar da goyon bayan ta ga babban bankin Najeriya (CBN) don sake fasalin takardun kudi na N1,000, N500 da N200.
Majalisar ta yi wannan kudiri ne bayan zazzafar muhawara kan kudirin da Sanata Uba Sani ya gabatar kan manufar CBN na sake fasalin kudin Naira uku