Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya fita kasar nan zuwa kasar waje yankin turai.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mista Paul Ibe, mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yada labarai, a cikin wata sanarwa mai taken “Atiku ya tafiya Turai ne a kan kasuwanci,” ya ce furucin da aka yi na cewa tafiyar ta ganin likitoci ce ba daidai ba ne.
Ibe ya ce “Atiku Abubakar zai tafi Turai da yammacin yau don ziyarar kasuwanci.”
Karanta kuma: An Nada Wike A Kwamitin Yakin Neman Zaben Shugaban Kasa Na PDP
Jaridar Daily Trust ta rawaito A Wani bangare na sanarwar ya ce “zai yi tafiya nan take bayan ganawarsa a ranar Juma’a a Legas, tare da jagorancin kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) tare da dan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP, Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta.
“Tafiyar yauci gaban tafiyar kasuwanci ne a baya na makonni 3 da suka gabata. A karshen ziyarar tasa au Turai, tsohon mataimakin shugaban kasar zai kuma yi amfani da damar wajen ziyartar iyalansa a Dubai.
“Tafiyarsa don kasuwanci ne da dalilai na dangi kuma ba shi da alaƙa da likitocin kamar yadda ake zargi a wasu ɓangarori.” Ibe yace.
A wani labarin kuma: Mun Gano Dimbin Dalibai Daga Kasashen Waje Da Ba Su Cancanta Ba – NYSC
Hukumar kula d masu yi wa kasa hidima (NYSC) ta ce a lokacin shirye-shiryen daukar yan Batch ‘B’ I da II na shekarar 2022, jami’ai sun gano adadi mai yawa na masu yiwa kasa hidima musamman wadanda ke da’awar samun horo a kasashen waje, tare da gazawar da suka yi na kare ilimin da ake zaton sun cancanta.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Babban daraktan hukumar NYSC, Brigediya janaral Mohammed Kaku Fadah, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis din nan a Abuja wajen bikin bude taron karawa juna sani na yan Batch C na shekarar 2022.