Babbar Kotun masana’antu ta kasa ta dage ci gaba da sauraron karar da gwamnatin tarayya ta shigar tana kalubalantar yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) ke ci gaba da yi zuwa ranar Litinin 19 ga watan Satumba domin sauraron karar da gwamnatin tarayya ta shigar.
A zaman da aka koma ranar Juma’ar nan, lauyan gwamnatin tarayya, James Igwe, ya bukaci kotun da ta gaggauta sauraron karar saboda gaggawar da aka yi domin baiwa dalibai damar komawa makaranta.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Igwe ya shaida wa kotun cewa tun da dai maganar ta riga ta shiga kotu, zai dace a janye yajin aikin har sai an yanke hukunci.
Karanta kuma: Kotu Ta Dage Shari’ar Gwamnatin Tarayya Da ASUU
Gidan talabijin na Channels ya rawaito cewa, Lauyan kungiyar ta ASUU, Femi Falana, ya ce an dage batun zuwa ranar Juma’a don ci gaba da magana ba don saurare ba. Ya ce an ba shi umarnin shiga tsakani da Gwamnatin Tarayya.
Falana ya kara da cewa a halin yanzu ASUU na ganawa da masu ruwa da tsaki domin ganin an shawo kan wannan rikicin da ya dabaibaye shi. Ya kuma roki Gwamnatin tarayya da ta ba su hadin kai domin magance matsalar.
Mai shari’a Polycarp Hamman, daga baya ya dage sauraron karar zuwa ranar Litinin 19, ga watan da muke ciki na 2022.
A wani labarin kuma: Atiku Ya Fice Daga Najeriya Bayan Ya Kaddamar Da Tawagar Yakin Neman Zabensa
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya fita dakga kasar nan zuwa waje yankin turai.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Mista Paul Ibe, mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yada labarai, a cikin wata sanarwa mai taken “Atiku ya tafiya Turai ne a kan kasuwanci,” ya ce furucin da aka yi na cewa tafiyar ta ganin likitoci ce ba daidai ba ne.