Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar a ranar Talatar nan ya ziyarci jihar Enugu inda ya sake jaddada alkawarin sake gina kasar.
Atiku, wanda tsohon mataimakin shugaban kasa ne, ya samu rakiyar mataimakinsa Gwamna Ifeanyi Okowa na jihar Delta a ziyarar ga masu ruwa da tsakin jihar.
KARANTA KUMA: Atiku Zai Samu Kashi 65 Cikin 100 Na Kuri’un Jihar Benue
Ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Akamu Ibiam inda ya samu tarba daga mai masaukin baki Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi da sauran mabiyan jam’iyyar.
A wani taron da ya yi da masu ruwa da tsaki, Atiku ya sake nanata soyayyar sa ga Ndigbo wanda ya ce shi ya sa ya zabi mazan Igbo a matsayin abokan takararsa a 2019 da kuma zaben badi.
Baya ga haka, ya tabbatar musu da kudirinsa na sake fasalin Najeriya da dora tsarin mulki kan gaskiya.
A wani labarin kuma: Farfado Da Jirgin Da Muka Gada Ba Kawai Siyasa Bane, Inji Gwamnan Jihar
Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Ezenwo Wike, ya ce farfadowa da dawo da dukiyoyin da ake ganin an rasa a jihar; jirgin saman Legacy 600, gaskiya ne, wanda ya wuce siyasa kawai.
Gwamna Wike ya bayyana haka ne bayan ya karbi jirgin Legacy 600 da ya sauka a yammacin ranar Talatar nan a filin jirgin sama na Fatakwal, Omagwa a karamar hukumar Ikwerre ta jihar.