By Abbas Yakubu Yaura
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da abin daya kira harin gaira babu dalili da wasu ‘yan daba suka kai wa majalisar dokokin jam’iyyar PDP reshen jihar Zamfara.
“Yana mai cewa wannan mummunan lamari ne ga dimokuradiyya da gudanar da zabe mai inganci a kasar.
Da yake mayar da martani kan lamarin ta ofishin yada labaransa dake Abuja, Atiku yace babu hujjar mumunar harin da ‘yan daba ke kaiwa ‘yan jam’iyyar adawa, inda yace bai kamata shugabannin jam’iyya mai mulki su amince da irin wadannan miyagun ayyuka ba.
A cewar Atiku, irin wannan rashin bin doka da oda da ake zargin magoya bayan jam’iyya mai mulki ke yi, wata gayyata ce ga tashe-tashen hankula da ka iya haifar da yanayi da zai sa a yi zabe mai cike da wahala.
Tsohon mataimakin shugaban kasan ya yi kira ga sufeto-Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, daya dauki matakin gaggawa don ganin an kama tare da gurfanar da wadanda ke da hannu a harin da aka kaiwa ‘yan PDP da magoya bayan jam’iyyar PDP na jihar Zamfara.
Kazalika Atiku ya ce, “Ya kamata ‘yan sanda su kasance ba tare da bin doka da oda a kasar nan ba, don kada ‘yan jam’iyya mai mulki su rika tunanin sun fi karfin doka.”