A yau Litinin ne bangarorin dake yaki da juna a kasar Habasha za su yi wani zaman tattaunawa domin nemo hanyar magance yakin basasar da aka kwashe tsawon shekaru biyu ana gwabzawa.
BBC ta ruwaito cewa, Zaman Wanda Kungiyar kasashen nahiyar Afrirka ce ta shirya shi, zai samu halartar wakilan gwamnati da na ‘yan tawayen Tigray da za su hallara a Afrirka ta kudu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dara Taci Gida: Mayakan ISWAP Sun Farmaki Na Boko Haram, Da Dama Sun Mutu
Idan za’a iya tunawa yakin ya sake barkewa ne a cikin watan Agustan shekarar nan bayan karya jarjejeniyar tsagaita wuta da bangarorin biyu su ka yi.
Yakin dai yayi mummunan tasiri matuka yayin da ake kyautata zaton cewa, an kashe dumban dubatan mutane, inda milliyoyin mutane suka rasa abinci da ababen more rayuwa.
Dimokuradiyya ta ruwiato cewa, Mayakan Tigray sun ce tawagarsu ta isa Afirka ta Kudu kuma abubuwan da suka sa gaba a ciki sun hada da dakatar da kai hare-hare nan take, da dawo da kai kayayyakin agaji da kuma janye sojojin Eritriya wani abu da kasashen duniya ke yi.
Sai dai Gwamnatin kasar ta Habasha ta ce ta kuduri aniyar samar da zaman lafiya amma ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare domin kula da filayen jiragen sama a yankin.
A WANI LABARIN KUMA: Yanzu-Yanzu: Rishi Sunak Ya Zama Sabon Firaministan Burtaniya
Rishi Sunak ya zama sabon Firaministan kasar Burtaniya. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Idan za’a iya tunawa cewa Liz Truss, tsohuwar Firaministar kasar ta yi murabus, tana mai cewa ba za ta iya ci gaba da gudanar da aikinta ba da hada kan yan jam’iyyar masu ra’ayin rikau da ta zabe ta