A wani abin da ake ganin ci gaba da gwabzawa fada tsakanin su, mayakan kungiyar IS a karshen mako sun kai hari a yankunan ‘yan Boko Haram, inda aka ce sun kashe shida daga cikinsu. Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito
A wani samame da ISWAP ta kai a sansanin ‘yan Boko Haram da ke Gajibo, wani gari mai tazarar kilomita 95 daga arewa maso gabashin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, sun kashe wasu 6 da suka ayyana a matsayin “kafirai”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Rishi Sunak Ya Zama Sabon Firaministan Burtaniya
A cewar Zagazola Makama, mai sharhi kan harkokin tsaro a tafkin Chadi, maharan sun kuma kwato bindigogin AK47 guda biyar daga hannun ‘yan ta’addan na Boko Haram.
ISWAP dai ta sha kai hare-hare da dama a kan ‘yan ta’addar Boko Haram a cikin rigingimun da suke ci gaba da yi, wanda ya janyo hasarar rayuka da dukiyoyi.
Tabarbarewar fadace-fadacen da ake yi tsakanin kungiyoyin masu ikirarin jihadi, na iya kai su ga halakar da ba za a iya jurewa ba, kamar yadda kungiyar ISWAP mai tayar da kayar baya ta sha alwashin fafatawa da mambobin tsohuwar kungiyarta fiye da ma sojojin Najeriya.
A WANI LABARIN KUMA: Ba Zan Yi Wa Atiku Yaki Neman Zabe Ba Saboda Abu Ɗaya, Gwamna Wike
Gwamna Nyesom Wike na jihar Rivers ya ce ba zai yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar yakin neman zabe ba, saboda ya nada makiyan jihar a kwamitin yakin neman zaben sa.
Majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ce ya yi wannan jawabi ne ga masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da magoya bayansa a Fatakwal yayin bikin kaddamar da gangamin yakin neman zaben jam’iyyar PDP na jihar Rivers a ranar Litinin.