Kungiyar Tarayyar Afirka ta sanar da sabon ranar da za a gudanar da tattaunawar zaman lafiya tsakanin bangarorin Habasha da ke rikici da juna da za a yi a kasar Afirka ta Kudu.
BBC ta ruwaito cewa, Mai bada shawara na musamman ga firaministan kasar Habasha kan harkokin tsaro, Redwan Hussien ne ya bayyana.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ba Mu Da Tabbacin Ko Gwamnatin Nan Ta Cimma Burin Yan Najeriya – Aisha Buhari
Tun da farko dai an shirya gudanar da tattaunawar ne a farkon wannan wata amma ba a samu yin zaman ba kamar yadda aka tsara.
A cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Hussien ya ce a yanzu za a gudanar da tattaunawar da kungiyar ‘yan tawayen Tigrai ne a ranar 24 ga watan Oktoban shwkarar nan, kuma ya tabbatar da cewa, Bangaren Gwamnatin kasar na Habasha zai halarci taron..
Ya kara da cewa, Gwamnatin Habasha ta ji takaicin yadda wasu ke dagewa wajen share fagen tattaunawar zaman lafiya da yada zarge-zargen karya kan matakan kariya.”
Sai dai harkawo hada wannan rahoton, bangaren yan tawayen Tigray ba ta ce uffan ba kan sabuwar ranar zaman Sulhun, amma a baya ta yi maraba da tattaunawar sulhu da gwamnatin Kasar.
A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da gwabza kazamin fada a cikin yakin basasar da aka kwashe shekaru biyu ana gwabzawa da sojojin gwamnati ln Habasha, Inda bangaren Gwamnatin suka kara kwace garuruwa uku a arewacin yankin Tigray daga hannun ‘yan tawayen.
A ranar Litinin, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres, ya ce “halin da ake ciki a Habasha na kara ta’azzara” ya kuma yi kira da a sake komawa kan Teburin sulhu cikin gaggawa.
Ko a A farkon wannan makon, shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Tedros Ghebreyesus, dan kabilar Tigrai, ya yi gargadin cewa lokaci yayi da za a kaucewa “kisan kare dangi a kasar”.
Idan ba manta ba abaya an shirya zaman sulhun ne karkashin jagorancin kungiyar ta AU a ranar 8 ga watan Oktoban shekarar nan, amma an dage shi daga bisani, saboda batutuwan da suka shafi kayan aiki da fasaha, a cewar jami’ai kungiyar ta AU.
A WANI LABARIN KUMA: Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Ya Yi Sabbin Nadi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dr Pokop Bupwatda a matsayin sabon babban daraktan kula da lafiya (CMD) na asibitin koyarwa na jami’ar Jos (JUTH).
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mista Ahmadu Chindaya, mataimakin darakta sashen yada labarai da hulda da jama’a na ma’aikatar lafiya ta tarayya ya fitar ranar Alhamis din nan.