Wani ma’aurata sun rabu bayan matar ta ki ba mijin takardun gidan da ta gada a wurin mahaifinta da ya rasu, gistreel.com ta ruwaito.
Matar ta gaji gida ne daga mahaifinta wanda bayan ta yi aure, mijinta da ‘yan uwansa su ka nace sai ta bar wa mijin takardun gidan.
KU KARANTA: Budurwa ta sharara wa saurayinta mari, ta ƙi amsar tayin aurensa, ta buƙaci ya zage damtse
Ikenna Ronald ya wallafa labarin a Twitter inda yace:
“Ina da wata kawa da mahaifinta ya bar mata gida a Ikoyi. Bayan ta hadu da wani saurayi dan talakawa, bayan watanni hudu da aurensu su ka rabu.
“A watan farkon aurensu, shi da ‘yan uwansa su ka matsa akan lallai sai ta bar masa gidan gadonta saboda shi ne “Shugaban Gida”. Wannan lamarin ne ya raba su.”
Yarinya ta shiga tsakanin iyayenta bayan lura da su na son keɓewa su mori tagomashin aurensu
Wani bidiyo mai ban dariya ya bayyana yadda ‘yar karamar yarinya ta shiga tsakanin iyayenta da alamun kishi tattare da ita, Legit.ng ta ruwaito.
An ga inda yarinya ta ke ta kuka da alamar ta yi matukar hassala bayan ganin sun kebe sun bar ta, hakan yasa tayi yunkurin maye gurbin mahaifiyarta.
An ga yadda iyayen nata su ka makale wa juna wanda hakan ya fusata yarinyar inda tayi gaggawar fashewa da kuka.