Limamin Masallacin Juma’a na Gadon Ƙaya, Imam Ali Yunus, ya shawarci Musulmai da su riƙa yi wa watan Ramadan tanadi tun kafin zuwansa.
Imam Yunus ya faɗi hakan ne a wata hira da ya yi da Freedom Radio a Jihar Kano a yau Talata, wanda Daily Nigerian Hausa ta saurara.
A cewar Limamin, duk da cewa al’umma s Nijeriya na fuskantar matsalar matsin rayuwa, za su iya yin tanadi na musamman domin tarbar watan mai alfarma.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Malami Ya Bayyana Aniyar Sa Ta Tsayawa Takarar Gwamnan Jihar Kebbi
Imam Yunus ya ƙara da cewa, a ƙasashen Larabawa, har kuɗi su ke ajiye wa duk wata a asusu domin tanadar watan Ramadan, inda ya ce “mu ma a nan Nijeriya duk da a na cikin matsalar tattalin arziki, za mu iya daure wa mu riƙa ajiye wani abu domin watan Ramadan.”
“Komai wahala da kunci za mu iya daidai gwargwado,” in ji shi.
Limamin ya kuma shawarci al’ummar Musulmi da su riƙa sauke nauyin iyalan su kafin su je ga mutane na waje.
“Sai mun fara yi wa iyalan mu hidima, sannan ƴan uwa sai kuma mutanen garin. Mu daure mu riƙa yi wa Ramadan tanadi na musamman janar yadda kasashen waje su ke yi, musamman irin su Saudiya.
“Ya kamata iyalan mu su ga canji a wajen abinci da kudin cefane saboda zuwan Ramadan,” in ji Imam Yunus.