Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Kabiru Gaya, ya dage cewa sabanin rahotannin da ake ta yadawa,cewa abar mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a baya a wajen kafa kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC ba haka batun yake ba.
Gaya, wanda ya rike mukamin Darakta-Janar na kungiyoyin goyon bayan Osinbajo a lokacin da mataimakin shugaban kasa ya nemi tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, ya shaida wa manema labarai a Kano cewa Osinbajo ya ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da aniyar dan takarar jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu.
KARANTA WANNAN LABARIN: ‘Yan Sanda Sun Kama Masu Aikata Muggan Laifuka Da Dama A Jihar Adamawa
Ya ce, “Ni dan kungiyar yakin neman zaben Tinubu ne, don haka batun mayar da kowa gefe bai taso ba. Hatta shugaban kasar ya ce yana son Osinbajo ya kasance tare da shi wajen tafiyar da al’amuran kasar don tabbatar da mika mulki ba tare da wata matsala ba.
“Babu wani abu kamar mayar da Osinbajo a gefe domin bayan zaben fidda gwani muna gidan Osinbajo lokacin da Tinubu ya zo ya ce yana bukatar goyon bayanmu. Mun yi tattaunawa sama da awa biyu. Suna aiki tare. Bai kamata siyasa ta raba mu ba”.
Gaya wanda ke neman komawa kujerar sa a jam’iyyar a karo na 5, ya ce yana da kwarin gwiwar cewa a jihar Kano, jam’iyyar APC za ta lashe kuri’u a dukkan kujerun zabe, yana mai hasashen jam’iyyar NNPP za ta zo ta biyu yayin da jam’iyyar PDP ce za ta zo ta uku.
Gaya ya ce APC ba ta damu da yadda jam’iyyar NNPP ke kara karfi ba, yana mai cewa za ta raba kuri’u na PDP ne kawai.
A wani labarin kuma, Dalilan Da Yasa Har Yanzu Ban Fitar Da Manufofina Ba— Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi, ya bayyana dalilin da ya sa aka samu jinkiri wajen fitar da takardar kudurinsa na zaben shugaban kasa a 2023.
Obi ya bayyana cewa “yana jiran matsayar kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, da kuma kungiyar TUC, kafin ya fitar da takardarsa.