Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party, LP, Peter Obi, ya bayyana dalilin da ya sa aka samu jinkiri wajen fitar da takardar kudurinsa na zaben shugaban kasa a 2023.
Daily Post ta ruwaito cewa, Obi ya bayyana cewa “yana jiran matsayar kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, da kuma kungiyar TUC, kafin ya fitar da takardarsa.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yan sanda Sun Kama Masu Aikata Muggan Laifuka Da Dama A Jihar Adamawa
Tsohon gwamnan jihar Anambra ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da BBC.
An soki dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP da jinkirta fitar da sanarwar manufofinsa a zaben shugaban kasa na 2023.
Amma, tsohon gwamnan ya yi watsi da sukar, yana mai jaddada cewa kasar na da ra’ayoyi da yawa da kuma rubuce-rubucen, tsare-tsaren wadanda suka kasa yin tasiri sakamakon rashin aiwatar da su da kuma niyyar gudanar da su a siyasa.
Babban daraktan yakin neman zaben shugaban kasa na Peter Obi, Doyin Okupe, ya bayyana cewa za a gabatar da taron jam’iyyar Labour ‘wani lokaci a mako mai zuwa’ inda ya kara da cewa zai sha bamban da na sauran jam’iyyun siyasa.
A WANI LABARIN KUMA: Garin Yin Ninkaya, Ruwa Ya Tafi Da Dan Shekara 16 A Bayelsa
Al’ummar Igbogene da ke karamar hukumar Yenagoa ta jihar Bayelsa sun shiga cikin zillumi a yammacin ranar Litinin, yayin da wani yaro dan shekara 16 mai suna Temedi Agbede Yerimene ya nutse a cikin ruwan da ya mamaye yankin.
Daily Trust ta ruwaito cewa, Yerimene ya tafi ninkaya ne a kofar shiga cibiyar kula da lafiya ta jihar a lokacin da ruwan ya tafi da shi