Dan wasan Najeriya Victor Osimhen ba zai ce a’a ga Real Madrid ba idan tayin da ya dace ya fito daga kungiyar ta kasar Spain.
A cewar rahotanni daga Italiya da Spain, Madrid na kallon dan wasan na Najeriya a matsayin shirin B idan sun kasa siyan Erling Haaland a lokacin bazara, tare da dan kasar Norway na sha’awar canja wurin wasu kungiyoyin Turai da suka hada da Barcelona da Paris Saint-Germain.
Gwamnatin Kano ta Kori wasu ma’aikata saboda badakalar Filaye
Majalisa tayi Watsi da kudurin warewa Mata kujeru na musamman
Haaland yana daya daga cikin manyan ‘yan wasan da kungiyar ta Spaniya ke nema, amma a cewar rahotannin baya-bayan nan, da alama za su nemi dan wasan a bazara mai zuwa, bayan sun ba shi shawarar ya kara kakar wasa daya tare da Borussia Dortmund.
Tuni dai shugaban Napoli Aurelio De Laurentiis ya kiyasta cewa dan wasan Najeriyar ya kai Yuro miliyan 100, farashin da Madrid din ba za ta iya biya ba, a cewar dan jaridar Italiya Fabio Santini.