Gwamnatin jihar Kano ta sanar da korar wasu ma’aikatan hukumar ƙasa da safiyo na jihar sakamakon samun su da laifin yin takardun jabu tare da sayar da wasu filaye mallakin hukuma.
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano, Muhammad Garba ya fitar a yammacin Alhamis.
Duba Wannan: https://dimokuradiyya.com.ng/majalisa-tayi-watsi-da-kudurin-warewa-mata-kujeru-na-musamman/
Sanarwar ta ce kwamitin bincike da aka kafawa ma’aikatan ya gano cewa ma’aikatan sun yi amfani da takardun jabu da kuma sayar da filayen gwamnati wanda hakan ya saɓa da dokar aikin gwamnatin jihar Kano.
Ma’aikatan da abin ya shafa sun haɗa da Abdulmuminu Usman Magami, mai matakin albashi na 6 da Abdullahi Nuhu Idris mai matakin albashi na 10 da kuma Audu Abba Aliyu mai matakin albashi na 05.
Sauran wanda da abin ya shafa ya haɗa da Baba Audu mai matakin albashi na 13.
A ƙarshe sanarwar ta ja hankalin ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da su kasance masu bin doka da oda.