- Gwamnatin Osun ta karyata labarin da ake yadawa na daukar aiki a ma’aikatun gwamnatin jihar
- Gwamnati ba ta daukar kowane irin aiki a ma’aikatun gwamnati
- Ya kamata jama’a su yi watsi da bayanan sannan kuma su kai rahoton duk wani yunkuri na zamba da sunan gwamnatin jihar ga hukumomin da suka dace
Gwamnatin Osun ta karyata labarin da ake yadawa na daukar aiki a ma’aikatun gwamnati, inda ta ce yaudara ce kawai, Vanguard ta rahoto.
Malam Olawale Rasheed, mai magana da yawun gwamna Ademola Adeleke ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Osogbo.
KARANTA WANNAN: Gwamna Fintiri Ya Raba Kayan Tallafin Rage Radadi Ga Marasa Galihu
Ya ce jihar ba ta daukar kowane irin aiki a ma’aikatun gwamnati.
Rasheed ya bukaci jama’a da su yi watsi da bayanan sannan kuma su kai rahoton duk wani yunkuri na zamba da sunan gwamnatin jihar ga hukumomin da suka dace.
“Gwamnatin Osun na son sanar da jama’a cewa a halin yanzu ba ta daukar wani aiki a hukumar ma’aikata ta jihar.
“Duk wani bayani da ke yawo a kafafen sada zumunta ko wasu kafafen sadarwa na daukar ma’aikata da sunan Gwamnatin Osun karya ce kuma yaudara ce.
“Akan batun sayar da fom da hukumar da’ar ma’aikata ke yi, ya kamata a tunatar da jama’a cewa karbar fom din aiki abu ne da aka saba da shi a duk hukumar kula da ma’aikata.
“Irin wannan aikin na yau da kullun ba alama ce ta cewa gwamnatin jihar ta fara daukar ma’aikata ba,” in ji shi.
Rasheed ya kara da cewa: “An shawarci jama’a da su yi watsi da irin wadannan bayanai, su kuma kai rahoton duk wani yunkurin damfarar su da sunan gwamnatin jihar Osun ga hukumomin da suka dace.
“Za a yi sanarwar ta tashoshin gwamnati a duk lokacin da gwamnati ta shirya fara daukar ma’aikata.
A wani labarin kuma, Majalisar Dokokin Wata Jiha Ta Hana ‘Yan Jarida Shiga Harabar Majalisar
Majalisar dokokin Ogun a ranar juma’a ta haramtawa ‘yan jarida shiga harabar majalisar domin gudanar da ayyukan su
Daukar matakin ya biyo bayan da majalisar dokoki ta umurci Akanta Janar na Jiha da wakilan kwamitin JAAC su gurfana gabanta domin yin karin haske kan zargin karkatar da kudaden kananan hukumomi
Wani dakataccen Ciyaman ya yi zargin cewa kananan hukumomi a jihar ba su da wani kaso daga asusun gwamnatin tarayya tun shekarar 2021
Majalisar dokokin jihar Ogun a ranar juma’a ta haramtawa ‘yan jarida da ke yada labarai a jihar shiga harabar majalisar domin gudanar da aikinsu na farko.
Jaridar Tribune Online ta tuna cewa Majalisar dokokin a ranar Alhamis ta umurci Akanta Janar na Jiha, Mista Babatunde Aregbesola, da wakilan kwamitin JAAC su gurfana gabanta a ranar Juma’a domin yin karin haske kan zargin karkatar da kudaden kananan hukumomi a kan gwamnatin Dapo Abiodun.