- Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri ya rabawa marasa galihu buhunan shinkafa 60,000 kowanne mai nauyin kilogiram 25
- Raba kayan tallafin na daga cikin kayayyakin rage radadin rayuwa da gwamnatin jihar ta tsara rabawa domin rage wahalhalun da ake fama da su a dalilin cire tallafin man fetur
- Kayan abincin da aka shirya sayar da su a kan kashi 50 cikin 100 tun da farko, yanzu za a rabasu kyauta ga mabukatan dake jihar
Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya baiwa marasa galihu buhunan shinkafa 60,000 kowanne mai nauyin kilogiram 25 a ranar Juma’a.
Shinkafar dai na daga cikin kayayyakin rage radadin rayuwa da gwamnatin jihar ta tsara rabawa domin rage wahalhalun da ake fama da su a dalilin cire tallafin man fetur.
KARANTA WANNAN: Majalisar Dokokin Wata Jiha Ta Hana ‘Yan Jarida Shiga Harabar Majalisar
Da yake kaddamar da rabon kayan abinci a yayin wani biki a Yola, babban birnin jihar, Fintiri ya sanar da cewa, kayan abincin da aka shirya sayar da su a kan kashi 50 cikin 100 tun da farko, yanzu za a rabasu kyauta gaba daya, wanda hakan zai bar jihar da kananan hukumomi daga tashin farashin kayayyaki.
“Musamman, mun fara rabon buhunan shinkafa 60,000 kyauta ga magidanta marasa galihu, ba tare da la’akari da bambancin jam’iyya ba,” inji gwamnan.
Ya kara da cewa ya kamata a mayar da ‘yan kwamitin kwantar da tarzoma na jiha da jiga-jigai a gefe a cikin tsarin rabon kayayyakin.
Ya kara da cewa tuni gwamnatinsa ta fara biyan N10,000 alawus na musamman ga ma’aikatan gwamnati da ’yan fansho a kowane wata, sannan ta raba tireloli kusan 100 na taki mai inganci ga ma’aikata da manoma, sannan ta sayi motocin bas na alfarma guda 10 don saukaka wahalhalun sufuri.
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su yi hakuri da gwamnatin jihar da ta tarayya kan tsadar kayan masarufi, domin a cewarsa yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine da kuma sauyin yanayi ya haifar da tsadar kayan abinci ba kawai a cikin kasa Najeriya ba amma duk duniya ne.
“Wahalhalun da ake fama da su a halin yanzu, musamman tsadar kayan abinci, ba wai kawai saboda cire tallafin man fetur ba ne ko kuma na musamman ga Najeriya; wasu daga cikin abubuwan sun hada da yakin Rasha da Ukraine da kuma sauyin yanayi,” inji shi.
A wani labarin kuma, Gungun ‘Yan Nijar Sun Yi Zanga-Zangar Neman Sojojin Faransa Su Fice
Jamhuriyar Nijar ta ba da kwarin gwiwa a ranar Juma’ar a wani mataki na gudanar zanga-zangar adawa da Faransa a karshen mako, a daidai lokacin da rikici ke kara tsami tsakanin sabbin shugabannin mulkin sojan kasar da abokan kawancen ta na gargajiya.
Gamayyar kungiyoyin farar hula da ke adawa da kasancewar sojojin Faransa a Nijar sun kira zanga-zangar zaman dirshan na kwanaki uku, daga yau Juma’a.