Fadar shugaban kasa a ranar Talata ya maida martani ga Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, bisa umurnin da ya bai wa Fulani makiyaya da su fice a dazukan jihar baki daya.
Sai dai a takardar da Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, ya ce shugaban kasar bai amince da wannan umurni ba, inda ya yi kira da a sassauta a tsakanin gwamnatin jihar da kuma Fulanin.
Fadar shugaban kasar ta ce; “a kokarin dakile ayyukan batagari, gwamnatin Ondo ba za ta kuma fice daga tsarin kundin dokokin Nijeriya ba”, ta lurantar.
Fadar shugaban kasar ta ce gwamnan wanda yake masanin dokoki, ya kamata ya sani cewa korar dubban Fulani makiyaya wadanda suka kwashe tsawon shekaru suna rayuwa a jihar bisa dogaro da ayyukansu wadansu batagari, sam bai dace ba.
Fadar shugaban kasar ta nemi gwamnatin jihar da Fulani makiyaya da su zauna su tattauna domin samun sulhu mai dorewa da zai samar da dawwamammen zaman lafiya a jihar.