Ba na son zama ubangidan kowa – El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce ba ya sha’awar zama ubangida ga kowane gwamna a jihar.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron karawa juna sani na inganta aiki ga manyan jami’an gwamnati a jihar Borno, ranar Litinin.
KARANTA WANNAN LABARIN:Yaki: A shirye muke mu yi abin da ya kamata – Jawabin Isra’ila kan ramuwar gayya da Iran ta kai
El-Rufai ya ce sau biyar kacal ya ziyarci Kaduna tun bayan da ya bar mulki kusan shekara guda da ta wuce.
“Ba na son zama ubangida, shi ya sa ba na tsoma baki cikin abin da ke faruwa a Kaduna, ina son shi (gwamna) ya koya ya samu aikin da kansa.
“Abin da ba mu da shi shi ne shugabanci nagari, manyan abubuwan da ke tattare da ingantaccen shugabanci.
“Ya kamata shugaba ya samu mutanen kirki don samun aikin.
“Allah ne kadai zai iya yin komai da kanshi, komai girman kai a matsayinka na shugaba, za ka iya yin tasiri kamar mutanen da ke kusa da kai kuma shi ya sa ake cewa babu wata kasa da ta fi ingancin ayyukansa na gwamnati,” inji shi.
A wani labarin kuma:Yanzu-Yanzu: An dakatar da Ganduje daga Jam’iyyar APC
Mambobin Jam’iyyar APC na Mazabar Ganduje da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a Jihar Kano sun dakatar da Shugaban Jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje.
Majalisar zartaswar Mazabar Ganduje karkashin jagorancin Haruna Gwanjo ce ta bayyana hakan a lokacin da take ganawa da manema labarai a Kano ranar Litinin.