Yadda gwamnatin Najeriya ta ceto mutane sama da 1000 da aka sace ba tare da biyan kudin fansa ba – NSA
Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin tarayya ta ceto sama da mutane 1,000 da aka yi garkuwa da su a fadin kasar nan ba tare da biyan kudin fansa ba.
Mista Ribadu ya bayyana haka ne a ranar Litinin a Abuja yayin da yake karbar dalibai 22 da aka ceto da ma’aikatan Jami’ar Tarayya ta Gusau, inda ya ce an gudanar da ayyukan a boye a cikin ‘yan watannin da suka gabata.
KARANTA WANNAN LABARIN:Da Ɗuminsa: An samu ƙaruwar hauhawar farashin kaya da kaso 33.20% a Najeriya
Ya ce ayyukan ceton da aka samu sun shaida kokarin gwamnati na kubutar da duk wadanda ake tsare da su ba bisa ka’ida ba.
“Ya zuwa yanzu mun saki sama da dubun irin wadannan mutanen ba tare da hayaniya ba tare da mutunta sirrinsu da amincin su.
“Mun sako mutane daga jihohin Zambara, Sokoto, Kaduna, Katsina, Taraba, Adamawa, da sauran jihohi da dama.
“Dubban, amma ba a ce uffan ba kuma mun gode wa Allah a kan hakan, kuma watakila wannan shi ne dalilin da ya sa muka samu nasara sosai.
“Wannan taron shine mataki na karshe a cikin jerin ayyukan ceto da muka yi a cikin ‘yan watannin da suka gabata don ‘yantar da wadanda aka yi garkuwa da su a baya-bayan nan da aka tabbatar.
“Yana kawo sauyi, lokaci ne kuma za mu ga sakamakon aikin da muke yi,” in ji shi.
A wani labarin kuma:Ba na son zama ubangidan kowa – El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce ba ya sha’awar zama ubangida ga kowane gwamna a jihar.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wajen wani taron karawa juna sani na inganta aiki ga manyan jami’an gwamnati a jihar Borno, ranar Litinin.