Hedikwatar rundunar yan Sandan Najeriya a daren ranar Talata ta ce ba ta da masaniyar wani matakin na tura jami’an ‘yan sanda zuwa gidan gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele a Abuja.
Da yake mayar da martani kan rahotannin da ke cewa ‘yan sanda na yin katsalandan a kan gwamnan CBN, jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Muyiwa Adejobi ya ce, “Ban san da wannan batu ba”.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mu Ba Mu Mamaye CBN Ba – DSS
An samu rahotannin cewa an ga jami’an ‘yan sanda sun killace gidan Maitama na gwamnan babban bankin kasar, Godwin Emefiele a daren ranar Talata.
Jami’an ‘yan sandan dauke da makamai an ce sun taso ne a lamba 8 a titin Colorado, Maitama, Abuja, wanda shi ne gidan gwamnan CBN.
A wani labarin kuma,’Wasu Mutane Suna Amfani Da Addini Don Tattalin Arziki, Siyasa’ — Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce wasu mutane suna fakewa da addini domin ci gaban tattalin arziki da siyasa.
Ya bayyana wannan a ranar Talata a Nouakchott, Mauritania, yayin da yake ganawa da Rashad Hussain, jakadan Amurka mai kula da ‘yancin addini na kasa da kasa.