Hukumar DSS ta musanta kai simame harabar babban bankin Najeriya a ranar Litinin.
Hukumar ta DSS ta bayyana rahotannin da suke bayyana cewa jami’anta sun shiga babban bankin kasar domin cafke gwamnan babban bankin kasa, Mista Godwin Emefiele, wanda ya dawo kasar da safiyar yau, a matsayin karya da wasu kafafen yada labarai suka tabbatar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Jami’an DSS Sun Mamaye CBN, Sun Datse Ofishin Emefiele
Sai dai wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar DSS, Dr Peter Afunanya ya aikewa Vanguard ta bayyana cewa jami’an DSS sun mamaye babban bankin na CBN da nufin cafke Emefiele a matsayin labarin karya.
Afunanya ya ce, “An jawo hankalin hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) kan labarin karya da ake yadawa cewa jami’anta sun mamaye babban bankin Najeriya tare da kama gwamnansa, a yau 16 ga watan Janairun 2023.
Sanarwar ta ce “Wannan labari ne na karya kuma yaudara ce.”
A wani labarin kuma, Jami’an Civil Defence Sun Kama Mai POS Da Zargin Hulda Da Yan bindiga
Hukumar tsaron fararan hulda da kaddarorin Gwamnati NSCDC reshen jihar Zamfara, ta ce jami’anta sun kama wani ma’aikacin POS mai suna Mustapha bisa zargin yin hada-hadar kudi ga ‘yan bindiga. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Kwamandan hukumar dake jihar, Muhammad Bello Muazu ne ya bayyana haka , a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, inda ya ce an kama mai laifin ne a yayin da yake yin wannan harkarlar a yankin Birnin Tsaba da ke karamar hukumar Zurmi ta jihar.