Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya gargadi kungiyoyi da masu neman tayar da zaune tsaye a Najeriya da su guji hakan domin biyan bukatun kansu.
Matawalle ya yi wannan gargadin ne a ranar Juma’a a Fatakwal a wajen bikin kaddamar da tuta na Babban Hafsan Sojin Ruwa na shekarar 2023.
Ya ce ina so in gargaɗi ƙungiyoyi ko mutane masu yada tashin hankali ta hanyar yada labaran karya ko kuma farfagandar ƙiyayya don su daina irin wannan.
Gwamnatin Tarayya ba za ta amince da duk wani mataki ko halayya da ka iya kawo barazana ga zaman lafiya a tsakanin ‘yan kasa masu bin doka da oda ba.
Matawalle, wanda ke mayar da martani kan yawaitar labaran karya da kalaman kyama da nufin haifar da rashin jituwa, ya kuma umurci jami’an tsaro da su kasance cikin shiri tare da magance duk wanda aka kama.
A wani labarin kumaYanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara ta Tabbatar da Zaben Abiodun, Ta Bada Umarnin Sake Sabon Zabe
Al’umma na cikin tsarin dimokuradiyya. Duk wani aiki da zai iya yanke shi ba za a amince da shi ba ya kara da cewa.
Ya kamata ‘yan kasa su girmama shugaban kasa; wanda hakan zai baiwa gwamnatinsa kwarin guiwar yin abin da ya kamata domin ganin kasar nan ta samu ci gaba. Ma’aikatar tsaro ba za ta lamunci duk wani aiki da zai kawo cikas ga zaman lafiya a kasar ba,” in ji ministan.