Hukumar shirya jarabawar WAEC a Najeriya ta ki sakin sakamako na dalibai daga jihohi takwas na tarayya da suka zana jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka ta 2023 sakamakon bashi da yayi wa Jahohin katutu.
Hukumar shirya jarabawar ta yammacin Afirka, WAEC,a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Legas ta hannun shugaban ofishin na kasa, Mista Patrick Areghan, yayin da yake ba da cikakken bayani kan sakamakon jarabawar da aka kammala kwanaki 44 da suka gabata.
Yayin da take bayyana kwarin gwiwar cewa wasu jihohin da abin ya shafa za su biya nan ba da dadewa ba, HNO ta bayyana Zamfara da Neja a matsayin wadanda suka fi yawan basussuka. Sai dai ya ki ambato sauran jihohin.
Amma Jihohin Zamfara da Neja ne suka fi kowacce jaha bashi,ya kuma kara da cewa daliban da suka kammala biyansu na kudi za su iya samun sakamakonsu a yanar gizon hukumar www.waecdirect.org.
KARANTA NANYakin Da Najeriya Ke Shiryawa Da Kasar Nijar Ba Alheri Bane-Zakzaky
Ina kara tabbatar da cewa sakamakon daliban jahohin da hukumar ke bi bashi ba za su fito ba a yanzu har sai sun biya,muna kira gare su da su yi hakan don baiwa makarantun da abin ya shafa damar samun sakamakonsu.
Ya yi bayanin cewa, a cikin mutane 1,613,733 da suka zana jarrabawar, 1,361,608, wadanda ke wakiltar kashi 84.38 cikin 100, sun samu kiredit da sama da haka a cikin mafi karancin darussa biyar.
Yayin da dalibai 1,287,920, masu wakiltar kashi 79.81 cikin 100, suka samu kiredit kuma sama da haka. mafi ƙanƙanta a darussa 5 da suka hada da Lissafi da Ingilishi
A yau, ina mai farin cikin sanar da ku cewa, an kammala dukkan hanyoyin da za a bi wajen fitar da sakamakon 2023 na jarrabawar kammala sakandare ta Afirka ta Yamma, WASSCE, na daliban Makaranta, 2023, a Najeriya
Ya kara da cewa, makarantun sakandire 20,867 da aka tantance a kasar ne suka gabatar da wadanda za su yi jarrabawar, yayin da dalibai daga wasu makarantu a jamhuriyar Benin, Cote d’Ivoire, da Equatorial Guinea da ake amfani da daftarin karatun sakandare ta Najeriya, su ma suka gabatar da wadanda suka cancanta.
ZAKUJI TUNDA FARKO CEWADa Dumi-Dumi: WAEC ta Fitar Da Sakamakon Jarabawar 2023
Areghan ya kara da cewa, a cikin jimillar dalibai, 794,280 maza ne, yayin da 819,453 mata ne, wanda ke wakiltar kashi 49.22 bisa dari da kashi 50.78 bisa dari.