Kungiyar likitocin Nijeriya ta bayyana matakin gwamnatin Nijeriya na sassauta dokar hana fitar da aka kafa a jihohin Legas, Ogun da kuma birnin Abuja saboda annobar Korona a matsayin kuskure, inda ta ce sam ba ta goyi bayan sassauta dokar ba.
A ranar litinin 27 ga watan Afrilu, yayin jawabi ga ‘yan Nijeriya, shugaban Buhari ya sanar sassauta dokar hana fitar a jihohin uku, matakin da ya ce zai soma aiki daga ranar 4 ga watan Mayu.
Sai dai cikin sanarwar da kungiyar likitocin Nijeriya ta fitar a baya-bayan nan, dauke da sa hannun shugabanta Dakta Franci Faduyile, ta ce a gaskiya matakin sassauta dokar ya yi wuri la’akari da cewar har yanzu akwai sauran rina a kaba dangane da karancin mutanen da ake yiwa gwajin kamuwa da cutar a rana ko mako guda, sai kuma karuwar adadin masu dauke da cutar da a kullum ake gani, adadin da a yanzu ya zarta dubu 2.