Babbar kotun tarayya za ta fara hutun Kirsimeti a ranar 29 ga watan Disamba mai kamawa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babbar jami’ar yada labaran kotun, Misis Catherine Oby Christopher, a ranar Litinin.
Sanarwar ta bayyana cewa hutun da ya yi daidai da tanadin doka mai lamba 46, doka ta 4 (C) na dokokin babban kotun tarayya, na shekarar 2019, zai kare ne a ranar 7 ga Janairu, shekarar 2022.
“Saboda haka, kotun ta ce za ta cigaba da zama a ranar 10 ga watan Janairu,” in ji sanarwar.
“Jama’a masu shigar da kara za su kasance da ‘yancin tunkarar kotunan da aka jera na aiki da ke kusa da su; ta farko Abuja, ta biyu Lagos, sai ta uku Port Harcourt.
A cewar sanarwar, Alkalai shida da aka nada domin gudanar da muhimman al’amura a lokacin hutun, su ne:
Justice Ahmed Mohammed da Zainab Abubakar (Abuja Division), Justice Daniel E. Osiagor da A.O. Awogboro (Lagos Division), da kuma, Justices A.T. Mohammed da S.I. Mark.
Bayan haka, kotun, a wata takardar da ke dauke da sa hannun babban alkalin kotun, Mai shari’a John Tsoho, ta ce taronta na shekarar shari’a na shekara-shekara na 2021/2022 da taron alkalai da na karshen shekara zai gudana ne daga ranar 14 ga Disamba zuwa 16 ga Disamba. 2021.
“A cikin shirin taron, za a gudanar da sabuwar hidimar godiya ta shekarar shari’a da zaman kotu a ranar Talata 14 ga Disamba, 2021, domin bikin fara ayyuka a kotuna a hukumance kamar yadda aka nuna a cikin da’ira.
“Bikin bude taron alkalai zai gudana ne a ranar Laraba, 15 ga watan Disamba, 2021 yayin da ake gudanar da bikin karramawar karshen shekara a ranar Alhamis 16 ga watan na Disamba 2021 da karfe 2:00 na rana.
Jaridar Dimukuradiyya ta rawaito sanarwar na cewa “Babban alkalin ya bayyana a cikin takardar cewa za a yi zaman kotu na musamman a ranar Litinin, 13 ga watan Disamba, 2021, domin girmama tsohon alkalin kotun, Marigayi Hon. Mai shari’a Adamu Abdu-Kafarati”, kamar yanda sanarwar ta bayyana.