Ministoci sha biyu ne suka ajiye kujerar sun a kasar Indiya, ciki hadda Ministan Lafiya dana Ilimi kamar yadda Jaridar Guardian ta wallafa
Hakan ya biyo bayan gyare-gyaren da Firaminstan Kasar Narendra Modi yayi kan irin juyin juya hali da cutar Covid-19 ta saka Kasar da kuma babban zabe dake tunkarar Kasar.
An dai ta korafe-korafe kan Ministan lafiya Harsh Vardham, musamman lokacin da annobar covi-19 ta yawaita a Kasar.
KARANTA:- Ba nida Shirin komawa APC: Kwankwaso
Mutane suna ta korafi asibitoci babu gadaje, ba Magunguna babu iskar gas.
Ravi Shankar Prasad, Ministan Shari’a shi kam yasha caccaka wajan kafafen yada labarai harda na kasashen ketare.
Anyi tsammanin Prasad zai kawo wani babban sauyi a tafiyar Modi amma babu wani sauyi daya gabatar.