Wadansu daliban Jami’ar Adekunle Ajasin University, dake garin Akungba a jihar Ondo sun gamu da hatsari a daidai shiga cikin jami’ar.
Hatsarin ya rutsa hatta ga wadanda suke kusa da wurin da hatsarin da ya auku.
Rahotanni sun ce hatsarin ya auku ne da misalin karfe shida na yammacin yau Asabar. Inda wani mai babban mota ya rasa burki ya hau kan karamar motan daliban.