Hukumar kwararrun a bangaren kudi NFIU, ta ce ba za ta sauya ka’idojin kayyade kudaden da ake fitarwa a farkon wannan wata ba.
Hukumar NFIU, a ranar 5 ga watan Janairu, ta umurci bankunan kasar nan da su daina aiwatar da bukatu na kudi daga asusun jama’a, da kuma biyan kudade marasa imganci da alawus-alawus na balaguro, daga ranar 1 ga watan Maris 2023.
Jaridar DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF) ta yi kuskure ga umarnin kuma ta yi wa hukumar mummunar fahimta game da sake duba ka’idojin fitar da kudade.
KU KARANTA KUMA Hukumar NFIU Ta Yi Harhadi Game Da Manufar Kayyade Cirar Kidi
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban manazarcinta kan harkokin yada labarai, NFIU, Ahmed Dikko, NFIU ta bayyana cewa, ta ba da isasshen lokaci ga dukkan hukumomi a kasar nan su rika fitar da tsabar kudi sama da ka’ida ta yau da kullum, kuma hakan baya cikin moriyar kasa da ‘yan kasa a ci gaba da yin irin wannan magana.
A cewar sanarwar, Daraktan Hukumar ta NFIU, Modibbo Hamman Tukur, ya bayyana a karshen ganawarsa da gwamnonin cewa hukumar a shirye take ta ba kwamitin mutum shida da aka kafa domin yin aiki da ita.
Modibbo ya ce: “Mun yi aiki cikin ayyukanmu da kuma doka. Mun fitar da ka’idojin da za a bi don shawo kan kwararowar binciken da muka ga zuwa Ka’idojin mu na nufin taimaka wa gwamnoni kada su yake su ko wani ma’aikacin gwamnati.
“Mun kai matsayin da idan muka bar abin da ke faruwa a yanzu ya ci gaba, duk cibiyoyin gwamnati za su shiga cikin KAYUADE FITAR KUDI A HANNU wasu kudade wanda bisa doka, ka’idoji da kyawawan ayyuka dole ne a ci gaba da binciken su wanda ba kyawawa ba ne kuma ba ma’ana ba.
“Muna jin cewa dole ne al’ummomi su ci gaba ta hanyar daidaita sauye-sauye da kuma daidaitawa ga sababbin ci gaba.”
Ya kara da cewa, a karo na karshe da NFIU ta fitar da ka’idojin kananan hukumomi, an kai su kotu amma sun ci nasara.
A Wani Labarin Kuma Daraktar Yakin Neman Zaben Dan Takarar Shugaban Kasa Tinubu, Ta Bar APC
Daraktar kungiyar farar hula ta kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa a jam’iyyar APC, Najatu Muhammad, ta fice daga jam’iyyar gabanin babban zaben 2023 mai zuwa.
Ta sanar da murabus din nata ne a wata takarda mai dauke da kwanan watan 19 ga watan Junairu 2023 ta kuma aikewa Sanata Abdullahi Adamu, shugaban jam’iyyar APC na kasa.