Babu wanda zai iya musuluntar da Najeriya — inji Fani-Kayode
Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode, ya ce Kiristoci ba su da wata fargaba da samun tikitin tsayawa takarar shugabancin kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki.
Ya tabbatar da cewa babu wanda zai iya musuluntar da Najeriya kamar yadda ake tsoro a bangarori da dama.
KARANTA WANNAN LABARIN:Sojoji sun Lakaɗawa Ƴan Sanda dukan tsiya kan kama Babur
Ya yi magana ne a shirin Siyasa a Yau, wani shiri na gidan talabijin na Channels.
Tsohon Ministan, wanda ya koma APC daga jam’iyyar PDP, ya amince cewa ya yi gargadin makircin gwamnati mai ci na musuluntar da Najeriya.
Sai dai ya ce ya yi addu’a game da lamarin kuma ya gane tikitin bangaskiya iri ɗaya ba shi da haɗari ga Kiristoci.