Sojoji sun Lakaɗawa Ƴan Sanda dukan tsiya kan kama Babur
Wasu sojoji da ke barikin Abalti, Surulere, jihar Legas, an yi zargin sun ci zarafin ‘yan sanda uku bisa kama wani mutum da har yanzu ba a tantance ko wanene ba, wanda aka kama da laifin karya dokar hana Okada da gwamnatin jihar ta kafa a yankin.
PUNCH Metro ta tattaro cewa mutumin, wanda ake zargin soja ne, yana kan Okada dinsa ne daura da Ojuelegba domin zuwa bariki, a lokacin da ‘yan sandan da ke aiwatar da dokar hana babur a yankin suka kama shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Garin Kanada Ya Gina Masallaci na Farko don riƙe Likitoci Musulmai
‘Yan sandan da suka hada da sufeto biyu, dan sanda da sauransu, sun kama shi tare da kama babur dinsa.
‘Yan sandan da ke aiki da sashin ‘yan sanda na Surulere, an ce suna shirin kai mutumin da babur dinsa zuwa ofishin, yayin da sojoji a kalla 20 suka far wa harabar.
Wata majiya da ta zanta da wakilinmu a ranar Alhamis, ta ce sojojin sun far wa tawagar ‘yan sintiri tare da raunata dan sandan da sufeto.
“Lokacin da suka isa wurin, sai suka fara kai wa ‘yan sandan farmaki har suka samu nasarar ‘yantar da mutumin da aka kama. Haka kuma sun kori ‘yan sandan babur din da aka kama suka tafi da shi.
“Mutumin da aka kama bai sanya kakinsa ba, shi da sojoji sun shiga barikin Abalti. Shi ya sa ake ganin shi ma soja ne. Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:30 na daren Laraba,” inji majiyar.
Majiyar ta ce sojojin sun kuma kwace wayar dan sanda da ke daukar hoton harin