Rundunar soji ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa zabukan 2023 za su gudana cikin kwanciyar hankali a jihohin Kudu maso Gabas da kowane bangare na kasar nan duk da barazanar da masu aikata laifuka ke yi. Kamar yadda Daily Post ta ruwiato.
Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Janar Lucky Irabor ne ya bada wannan tabbacin a Abuja a wajen bikin bayyana ayyukan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari karo na 25.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zabe: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Rufe Kwalejojin Kimiyya Da Fasaha
NAN ta ruwaito cewa, taron ya kunshi Ministan Tsaro, Bashir Magashi, wanda ya gabatar da sakamakon ma’aikatar.
Da yake amsa tambaya kan barazanar da bangaren Simon Ekpa na masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) ke yi na dakatar da babban zaben bana a jihohin Kudu maso Gabas, Irabor ya ce babu wani mutum ko kungiya da za ta iya hana zaben.
Ya ce: “Rundunar soji na aiki tare da ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro domin ganin an kawar da masu aikata laifuka daga kungiyar IPOB da kuma tsaro ta Gabas.
Irabor ya kuma tabbatar da matsayin Magashi cewa “babu wani yanki na Najeriya da ke karkashin ikon Boko Haram ko wata kungiyar ta’addanci.”
A cewarsa, an ‘yantar da dukkanin al’ummomin shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya daga ‘yan ta’adda.
A wani labarin kuma, Da Dumi-Dumi: Yan sanda Sun Cafke Faston Dake Wa’azi Dauke Da AK-47
Tawagar Rundunar ‘yan sandan dake bincike a yankin Garki, Abuja, ta tsare limamin cocin House on the Rock (Babin Abuja), Fasto Uche Aigbe, bisa laifin rike AK-47 a yayin da yake wa’azi.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike a kan Aigbe bayan wani faifan bidiyo da ya nuna shi dauke da AK-47 wanda ya yadu a shafukan sada zumunta.