Tawagar Rundunar ‘yan sandan dake bincike a yankin Garki, Abuja, ta tsare limamin cocin House on the Rock (Babin Abuja), Fasto Uche Aigbe, bisa laifin rike AK-47 a yayin da yake wa’azi.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike a kan Aigbe bayan wani faifan bidiyo da ya nuna shi dauke da AK-47 wanda ya yadu a shafukan sada zumunta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Zabe: Gwamnatin Tarayya Ta Bada Umarnin Rufe Kwalejojin Kimiyya Da Fasaha
Majiyar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa, ta samu labarin wani Insfekta mai suna Musa Audu ya mika wa Aigbe bindigarsa.
Kwamishinan ‘yan sanda reshen babban birnin tarayya, Sadiq Abubakar, ya bai wa Babban Sefeto janar na yan sandan kasa shawarar korar jami’in ‘Dan sandan, Insifekta Audu.
An bayyana cewa Audu zai fuskanci hukuncin shari’a saboda mika bindigarsa ga Faston Cocin House on the Rock, reshen Abuja, Uche Aigbe, ranar Lahadi.
A wani labari kuma, Yanzu-Yanzu: Jiga-Jigan Jam’iyar Labour Da Daruruwan Magoya Bayansu Sun Koma APC
A ranar Litinin Daruruwan ‘ya’yan jam’iyyar Labour Party (LP) ne a yankin Kudu maso Yamma, suka yayyaga katin zama mambobin Jam’iyar, inda suka kuma koma jam’iyyar APC domin marawa tafiyar Asiwaju Bola Tinubu, na ganin yayi nasara a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.
Wannan na zuwa ne sa’o’i kadan bayan Bashir Bashir, dan takarar gwamna na jam’iyyar Labour, ya gana da Tinubu a Abuja