Badaƙalar N585m: AGF ta musanta masaniya kan buƙatar Edu
Babban Akanta Janar na Tarayya (AGF), Dokta Oluwatoyin Madein, ta musanta batun sanin masaniyar rahoton bukatar biyan Naira miliyan 585.198 da ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Dr. Betty Edu ta yi.
Ministan ta bukaci ofishin Akanta-Janar na kasa da ya biya wadannan makudan kudi zuwa asusun ajiyar wata Oniyelu Bridget Mojisola.
KARANTA WANNAN LABARIN:Ɗauko hayar Peseiro babban kuskure ne – Gara Gombe
Bukatar Dr. Edu tana kunshe ne a cikin wata wasika da aka ambata: FMHAPA/HQ/S.208 da kwanan wata 20 ga Disamba, 2023.
Bayanin nata shi ne cewa an biya kudin ne don tallafi ga marasa galihu a jihohin Akwa Ibom, Cross River, Ogun da Legas.
Sai dai kuma da take mayar da martani kan cece-kucen da aka taso daga bukatar biyan kudaden da ake ganin haramtacce ne, kungiyar ta AGF ta ce ba ta mutunta wannan bukata ba domin ba alhakinta ba ne na biyan wasu ayyuka da shirye-shirye a madadin ma’aikatu da hukumomi (MDAs).
Matsayar Dr. Madein yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada labarai, Mista Bawa Mokwa na OAGF, ya fitar a Abuja da yammacin yau.
Ta bayyana cewa ana fitar da kason ga MDAs masu dogaro da kai daidai da kasafin kudin kuma irin wadannan MDAs ne ke da alhakin aiwatar da ayyukansu da kuma biyan kudaden irin wadannan ayyuka.
AGF ta bayyana cewa duk da cewa ofishinta ya samu wannan bukata daga ma’aikatar, amma bai aiwatar da biyan kudin ba.
Sai dai an shawarci ma’aikatar kan matakan da suka dace da za ta bi wajen biyan irin wadannan kudade daidai da tsarin biyan kudi da aka kafa.
AGF ta lura cewa a irin wannan yanayi, Ma’aikatun da abin ya shafa ne ke aiwatar da biyan kuɗaɗen a matsayin masu gudanar da lissafin kansu kuma ba za a biya kaso mai tsoka a asusun mutum ba da sunan Project Accountant ba
A wani labarin kuma:Tura Naira Miliyan 585 a wani asusu, ba’a saɓawa doka ba – Hadimin Betta
Rasheed Zubair, mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai da wayar da kan ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, Dr Betta Edu, ya ce kudin da aka fitar na Naira miliyan N585,189,500.00 a cikin wani asusu na kashin kai ya halatta kuma ya yi daidai da dokokin aikin gwamnati.
Edu a cikin wata takarda mai dauke da sa hannunta da kuma wadda ta mika wa ofishin Akanta-Janar na Tarayya, umarnin a raba kudaden ga wata Oniyelu Bridget Mojisola.