Tsohon dan majalisar dattawa daga jahar Kaduna dake Arewa maso yammacin Najeriya Sen Shehu Sani ya soki shugaba Bola Tinubu kan nada Mohammed Badaru a matsayin ministan tsaro.
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya ce bai kamata Tinubu ya nada dan siyasa a matsayin ministan tsaro ba ana cikin wannan yanayi na karancin tsaro a kasar.
Sani ya ce kamata ya yi a baiwa wani jami’in soja mai ritaya wanda yayi aikin soja kuma yasan minene tsaron kasa wanda kuma keda bayanan nasarorin da aka samu da wadanda ba’a samu ba.
KARANTA NAN“Ƴan Ta’adda na shirin kai hari ga Jirgin ƙasan Kaduna-Abuja nan ba da jimawa ba” ~ DSS
Sani ya rubuta a shafin Twitter cewa duba da kalubalen tsaro da kasar nan ke fuskanta, na ga ya kamata Ministan tsaro ya zama jami’in soja mai ritaya mai gogewa da kuma tarihin nasarori.
Wannan ofishin bai kamata ya zama siyasa kawai ba, musamman a wannan lokacin da mafi yawan mutanen kauyuka basu iya kwana da ido biyu a rufe.
Inda suke fargabar abkowar barayin daji da ke sace mutane don karbar kudin fansa ko kuma su Dave duk wani abinda ka mallaka Ba tare da wani ya hana su ba.
A WANI LABARIN KUMA
Mai Magana Da Yawun Matawalle Ya Bukaci Gwamna Dauda Lawal Da Ya Sauka Daga Mulki Tunda Bai Iyaba
Mai magana da yawun tsohon gwamnan jahar Zamfara Dr Muhammad Bello Matawalle ya yi kira ga gwamnan jahar na yanzu Dr Dauda Lawal Dare da ya gaggauta aje aiki saboda abinda ya kira rashin iya aiki na sabon gwamnan da mukarraban gwamnatinsa
Kaura yayi wannan magana ne a daidai lokacin da yan dashi da makami ke cigaba da cin karensu babu babbaka a fadin jahar ta Zamfara mai arzikin kasar noma.