Kakakin tsohon gwamnan jihar Zamfara, Kwamared Abdullah Anas Kaura, a ranar Laraba ya bukaci gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal da ya yi murabus, bisa zargin cewa jihar a halin yanzu tana fuskantar rudani sakamakon ‘rashin jagoranci’.
Ya bukaci Gwamna Lawal, da ya gaggauta sauka daga mulki. Kaura ya kuma yi zargin cewa wadanda ba ’yan asalin jahar ba ne sune masu rike da madafun iko.
Kuma sune ke tafiyar da al’amuran jihar, lamarin da ke haifar da rashin tsaro a yankin.
A cikin wata sanarwa da ya sanyawa hannu, kakakin ya kuma bayyana irin tsananin talauci da al’ummar jihar Zamfara ke fama da su. Ya kuma shawarci gwamnan da ya gaggauta daukar matakin magance matsalar talauci da rashin tsaro da ke kara ta’azzara a jihar.
KARANTA NANTinubu Ya Gaji Mawuyacin Tattalin Arziki daga Tsohon Shugaba Buhari – Oshiomole
Ta hanyar amfani da dabarun da aka yi amfani da su a lokacin gwamnatin da ta gabata, gwamnati mai ci a jihar Zamfara na da babbar dama ta magance talauci da rashin tsaro yadda ya kamata, Kaura ya jaddada.
Da yake nuna matukar damuwarsa kan karuwar talauci da jinkirin biyan albashi, Kaura ya yi kira ga gwamnan ya yi murabus, yana mai alakanta hakan da rashin iya aiki.
Kaura ya kuma lura da yawaitar sace-sace da kashe-kashe a cikin kankanin lokacin gwamnatin Lawal.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar Zamfara da su ci gaba da kasancewa da kyakkyawar dabi’a, musamman masu goyon bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar.
A WANI LABARIN KUMAMajalisar dokokin jihar Kwara ta ɗauri ɗamarar daƙile sayar da Jabun magunguna a Jihar
Ɗaya daga cikin hanyoyin farko na yaƙi da talauci shine ta hanyar samar da ayyuka masu yawa, musamman ga matasa. Ina kira ga al’ummar jihar Zamfara da su ci gaba da samar da zaman lafiya tare da marawa jam’iyya mai mulki baya a kokarinta na ganin an farfado da al’umma,in ji Kaura.