Bakuwar Cuta: Jihar Plateau Ta Musanta Batun Mutuwar Shanu 1,000
Gwamnatin jihar Filato ta musanta labarin da ake yadawa cewa sama da shanu 1,000 ne suka mutu sakamakon wata bakuwar cuta cikin kwanaki hudu a wasu kauyukan karamar hukumar Mangu ta jihar.
Daily Trust ta ruwaito a ranar Lahadin da ta gabata cewa an yi ta yada labari a shafukan sada zumunta da kuma a wasu jaridun kasar kan yadda aka ce an kashe shanu.
KARANTA WANNAN LABARIN:Dubban Musulmai Sun Gudanar da Addu’oin Neman Samun Ruwan Sama A Jihar Adamawa
Sai dai gwamnatin jihar Filato a wata sanarwa da daraktan yada labarai da hulda da jama’a ga gwamnan, Gyang Bere ya fitar, ta ce labarin ba gaskiya bane.
“An jawo hankalin gwamnatin jihar Filato kan wani labari da aka buga a wasu jaridun kasar nan kuma yana ta yawo a shafukan sada zumunta cewa sama da shanu 1,000 ne suka mutu sakamakon wata bakuwar cuta cikin kwanaki hudu a wasu kauyukan karamar hukumar Mangu ta jihar.
“Labarin da aka ce ya yi nisa da gaskiya, domin bai nuna gaskiyar abubuwan da ke faruwa a cikin al’ummomin da aka ambata ba a cikin labarin. Don kaucewa shakku, babu wani abu makamancin haka a yankin karamar hukumar Mangu kuma gwamnati ba ta samu labarin mutuwar dabbobi daga wata al’umma da aka ambata a reshen jihar ba.
A wani labarin kuma:Cambodia: Jonathan Ya Bukaci Shugabannin Duniya Su Nemi Zaman Lafiya Ta Hanyar Dimokuradiyya
Tsohon shugaban Najeriya Dakta Goodluck Jonathan ya bukaci shugabannin kasashen duniya da su nemi zaman lafiya ta hanyar bin tafarkin dimokuradiyya na gaskiya da kuma shugabancin son jama’a a kasashensu.
Dokta Jonathan ya kuma gabatar da wani batu na shugabanci nagari, wanda ya bayyana a matsayin ummul aba’isin tabbatar da kwanciyar hankali a siyasance da ci gaba.