Dubban al’ummar musulmi a karamar hukumar Hong da ke jihar Adamawa sun gudanar da addu’o’i na musamman don neman samun ruwan sama.
Karamar hukumar Hong ta kasance tana yankin arewacin jihar Adamawa ne inda ake samun karancin ruwan sama tun farkon saukar damina.
KARANTA WANNAN: Gwamnatin Wata Jiha A Najeriya Ta Saki Fursunoni 30 Daga Gidan Yari
A ci gaba da neman samun ruwan sama mai albarka daga Allah SWA a kewayen karamar hukumar dama jihar baki daya, a ranar Asabar ne al’ummar musulmi a birnin Hong suka hallara a wani fili a hedkwatar karamar hukumar da ke birnin Hong, inda suka gudanar da sallar Istiqa’a da kuma addu’o’i na musamman na neman ruwan sama.
Daily Post ta rahoto cewa mataimakin babban limamin masallacin Hong Central Sa’idu Garba ne ya jagoranci sallar tare da hakimin Hong Umar Mahmoud.
Sa’idu Garba ya yi addu’ar samun isasshen ruwan sama ga manoma domin samun amfanin gona mai yawa, ya kuma roki Allah ya kawo karshen wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta a duk inda suke zaune a fadin kasar nan.
A wani labarin kuma, Ko Kadan Gwamnatin APC ba ta damu da halin ‘yan Najeriya ba – Inji Wani Lauya
Lauya kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Dele Farotimi ya ce jam’iyyar All Progressives Congress, gwamnatin APC ba ta damu da talakawan Najeriya ba a tsarin tallafin da take yi.
Farotimi ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan talabijin na Arise a ranar Juma’a.