Kungiyar Manoman Albasa ta kasa a jihar Kebbi ta bayyana cewa; ta yi asarar Albasar da darajarta ya kai naira biliyan 1 sakamakon wata bakuwar cuta guda biyu da ta addabi ma’adanar Albasar a jihar.
Shugaban kungiyar, Alhaji Bello Uba, shi ne ya shidawa manema labarai hakan a Birnin Kebbi a ranar Laraba, inda ya ce akalla manoma 20, 000 ne wannan asarar ta shafa.
Ya ce: cutar kawai Albasar da aka adana ta farmaki ba, hatta irin Albasar da suke shukawa, sai da cutar ta barnata. Ya tabbatar da cewa ba su ta6a fuskantar wani abu makamancin haka ba tsawon shekaru masu yawa.
Ya kara da cewa manoman sun yi imanin cewa a halin yanzu babu maganin cutar da aka yiwa lakabi da ‘Zazzalau’ da ‘Raba.’
Shugaban kungiyar ya ce ya zuwa yanzu ba su sanar da gwamnati ba, ko wata hukumar gwamnati, amma za su yi gaggawar sanar da su nan ba da jimawa ba.